Sai dai masu wannan ra’ayi sun ci karo da turjiya daga wasu Jamusawa masu sassaucin ra’ayi da ke adawa da zanga-zangar a sauran biranen kasar.
Tun a watan Oktoba PEGIDA ke jagorantar zanga-zangar kyamar addinin Musulunci a Jamus duk da shugabar gwamnatin kasar Angela Merkel ta bukaci a dakatar da zanga-zangar.
Shugabannin Kiristoci da ‘Yan kasuwa da shugabannin siyasa a Jamus sun la’anci zanga-zangar da aka gudanar a biranen Berlin da Cologne da Stuttgart da Dresden.
Sai dai kuma masu zanga-zangar sun ci karo da dubban Jamusawa da suka kaddamar da zanga-zangar adawa da masu kyamar Musulunci.ABNA